Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Nada Wadanda Zasu Binciki Abubuwan Da Suka Wakana A Jenin - 2002-04-23


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya nada tawaga mai wakilai 3 domin binciken farmakin sojan da Isra'ila ta kai kan sansanin Falasdinawa 'yan gudun hijira na Jenin.

Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun gudanar da kashe-kashen gilla a sansanin dake yankin Yammacin kogin Jordan.

Wannan tawaga ta MDD, tana karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Finland, Martti Ahtisaari. Sauran membobin sune tsohon shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya, Cornelio Sommaruga da tsohuwar babbar jami'ar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Sadako Ogata.

Mr. Annan ya ce wannan kungiya zata tabbatar da abubuwan da suka faru ne kawai.

Ministan harkokin wajen Isra'ila, Shimon Peres, ya ce ba su aikata wani laifi ba.

Wakilin Falasdinawa a MDD, Nassar al-KIdwa, ya ce hukumomin Falasdinawa sun gamsu da tawagar, yana mai cewa manyan jami'anta uku mutane ne da aka sani da fadin gaskiya.

A halin da ake ciki dai, kungiyar kare hakkin bil Adam ta "Amnesty International" ta ce tana da shaida a hannunta cewar sojojin Isra'ila sun yi mummunar keta hakkin bil Adama a sansanin na 'yan gudun hijira da aka ragargaza shi.

XS
SM
MD
LG