Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ki Yarda Da Turjewar Isra'ila... - 2002-04-24


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya ce yana son tawagar binciken da majalisar zata aika zuwa sansanin 'yan gudun hijira na Jenin ta isa can zuwa ranar asabar.

Bayan wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhun MDD da aka gama dazu, Mr Annan ya yarda zai jinkirta tashin jami'an tawagar na wani dan lokaci kadan ta yadda zai gana gobe alhamis da wakilan kasar Bani Isra'ila.

Tun da fari a jiya talata, Isra'ila ta canja ra'ayi game da kyale masu binciken, da su gudanar da ayyukansu, tana mai cewa ba zata yarda su tafi can ba sai an kara fayyace irin ayyukan da zasu gudanar. Isra'ila ta ce zata hada kai da masu binciken, amma kuma tana son Mr. Kofi Annan ya sake duba wadanda ya nada, domin a sanya kwararru kan yaki da ta'addanci da ayyukan soja.

Haka kuma, Isra'ila tana son masu binciken su ziyarci sansanin na Jenin kawai, kada su shiga wani yankin dabam.

Amurka, wadda ta gabatar da kudurin tura tawagar, ta ce tana son ganin an aiwatar da wannan kuduri kamar yadda aka rubuta shi.

Wakilai uku da Mr. Annan ya nada a wannan tawaga suna karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Finland, Mr. Martti Ahtisaari. Sauran sune tsohon shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya, Cornelio Sommaruga, da tsohuwar babbar jami'ar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, Sadako Ogata. Tsohon hafsan sojan Amurka, Manjo-janar William Nash, mai ritaya, zai yi aiki a zaman babban mai bada shawara kan harkokin soja ga wannan tawaga.

Tawagar, zata binciki zargin da Falasdinawa suka yi cewa Isra'ila ta yi kashe-kashen gilla a cikin sansanin.

A yayin da ake wannan ne kuma, kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Amnesty International" ta ce wakilanta, wadanda komowarsu ke nan daga Jenin, sun samu kwakkwarar shaidar cewa sojojin Isra'ila sun yi mummunar keta dokokin kare hakkin Bil Adama na kasa da kasa. Kungiyar "Amnesty International" ta ce ya kamata wannan tawaga ta MDD da za a tura zuwa Jenin, ta zamo matakin farko kawai na cikakken binciken da ya kamata a gudanar kan abubuwan da suka faru a Jenin. Kungiyar ta ce idan ba a fayyace ma tawagar filla-fillar abubuwan da zata yi ba, kuma idan ba a bukaci cikakken hadin kai aka samu daga Isra'ila ba, to wannan tawaga ta MDD ba zata iya gudanar da bincike kammalalle kamar yadda ya kamata ba.

XS
SM
MD
LG