Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Kudi Daga Kasashe 44 Na Afirka Sun Gana Da Takwarorinsu Na Amurka... - 2002-04-24


Jami'an kudi na kasashe 44 daga yankin kudu da hamadar Sahara a nahiyar Afirka, sun hadu da takwarorinsu na Amurka a wani taron da ma'aikatar harkokin waje ta gudanar jiya talata a nan Washington, da nufin bunkasa zuba jarin sassa masu zaman kansu a nahiyar Afirka, ta hanyar fadada yin amfani da mizanin auna karfin karbar bashin kasa.

Kasashe kalilan ne kawai a nahiyar ta Afirka suke amfani da irin wannan mizani, wanda kamfanonin auna karfin karbar bashi masu zaman kansu ke zanawa.

Wakilin Muryar Amurka, David Gollust, wanda ya halrci taron, ya ce gwamnatin shugaba Bush ta nace kan cewa zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu ne kawai, ba wai agaji ba, mataki mafi nagarta na bunkasa kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Gwamnatin ta Amurka, ta shirya wannan taron a wani bangare na kokarin janyo hankalin gwamnatocin yankin na Afirka da su kyale kamfanonin auna karfin karbar bashi masu zaman kansu, su ringa duba littattafai da takardunsu na hada-hadar kudi, ta yadda za a san irin yadda tattalin arzikinsu ke gudana a zahiri, abinda kuma zai iya shawo kan masu zuba jari.

Wannan taro da aka yi shi kwana guda bayan tarurrukan Bankin Duniya da na Asusun Lamunin Kudi na Duniya a nan Washington, ya kunshi ministocin kudi da darektocin manyan bankunan kasashen Afirka 44, da kuma manyan jami'an gwamnatin Amurka, cikinsu har da sakataren harkokin waje Colin Powell, da Sakataren Baitulmali (watau ministan kudi) Paul O’Neill.

A cikin muhimmin jawabin da ya gabatar ga taron, Mr. Powell ya ce kashi 80 daga cikin 100 na kudi kimanin dala miliyan dubu 300 na jarin dogon lokaci dake kwarara zuwa kasashe masu tasowa a kowace shekara, yana fitowa ne daga aljihun sassa masu zaman kansu. Ya ce kasashen da suke da manufofin tattalin arziki masu nagarta, zasu samu karin agaji da jarurruka, yana mai fadin cewa kasashen da suke amfani da mizanin karfin karbar bashi, zasu samu fifiko kan sauran kasashe a gwagwarmayar neman jarin kasashen waje.

Mr. Powell ya ce duk kasar da take amfani da mizanin karfin karbar bashi, to tana da makamin samo jari daga waje, kuma yana iya zamowa hanyar da kasa zata ci moriya sosai daga tsarin tattalin arzikin duniya.

A yanzu haka dai, kasashen kudancin hamadar Sahara na Afirka hudu ne kawai suke yin amfani da irin wannan mizani. Kasashen sune Botswana da Mauritius da Senegal da kuma Afirka ta Kudu. Jami'an wadannan kasashe hudu, sun taka muhimmiyar rawa a tattaunawar da aka yi wurin wannan taro kan yadda kasa zata iya fara yin amfani da wannan mizani, ta kuma ci moriyarsa.

Gwamnatin shugaba Bush ta ce zata biya kudin auna karfin karbar bashin kasashe 10 daga aljihunta, a wannan tsari, ko aikin da za a kammala cikin shekara guda, watau na auna kasashen. Kamfanin auna karfin karbar bashin kasashe mai suna "Fitch Ratings Limited," daya daga cikin kamfanoni uku dake gudanar da irin wannan aiki a duniya, shine ya samu kwantarakin gudanar da wannan aikin, kuma yana daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin gudanar da wannan taro na Washington.

XS
SM
MD
LG