Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Daba Suna Yin Garkuwa Da Ma'aikatan Mai A Nijeriya - 2002-04-24


Kamfanin mai na Chevron-Texaco ya ce wata kungiyar matasa 'yan daba a Nijeriya ta sako mutane 44 daga cikin wasu ma'aikata 88 da take yin garkuwa da su a wani dandalin hakar mai dake cikin teku, kusa da gabar ruwan kasar.

Wani mai magana da yawun kamfanin, Fred Gorell, ya fada jiya talata cewa, ana ci gaba da tattaunawa domin a sako sauran ma'aikatan kamfanin su 43, wadanda 'yan ta-kifen suka tsare.

Ya nuna kyakykyawar fata cewa, bada dadewa ba za a sako sauran ma'aikatan, kuma ba tare da an raunata wani cikinsu ba.

Jami'an kamfanin man na Chevron-Texaco sun labarta cewa a ranar lahadin da ta gabata ce, wasu matasa su 20 suka hau dandamalin wannan rijiyar mai, ya zuwa jiya talata kuma, wasu karin matasan su kusan ashirin suka rufa masu baya.

Wannan rijiyar mai, tana tazarar kilomita 8 ce a cikin teku daga birnin Escravos dake gabar ruwa.

Ma'aikatan da ake yin garkuwa da su din, sun hada da wasu 'yan Nijeriya da kuma 'yan kasashen waje. Tsageran matasan dake tsare da su dai, sun ce, suna son a basu ayyukan yi ne a wanann rijiyar mai.

XS
SM
MD
LG