Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Nan Gaba Zata Gurfanar Da 'Yan Jaridar Kasashen Waje Gaban Kotu... - 2002-04-25


Gwamnatin Nijeriya ta ja kunnen 'yan jaridun kasashen waje cewar zata gurfanar da su a gaban kotu, idan sun buga abinda ta kira "rahotannin karya" a game da kasar.

Jiya laraba gwamnatin ta yi wannan gargadi a bayan wani rahoton da mujallar labarai ta Amurka mai suna "Time" ta buga. Rahoton ya ce jami'an gwamnatin Nijeriya sun yi kokarin bada cin hanci ga 'yan jaridun kasashen waje domin su ringa gyara labaran da suke bugawa game da Nijeriya.

Mujallar "Time" da aka buga a makon jiya, ta ce ministan yada labarai na Nijeriya, Jerry Gana, ya kira wani taro da wakilan kafofin yada labaran kasashen waje cikin watan Fabrairu a Abuja, domin yayi kukar rahotannin da gidan telebijin na CNN ya yada game da tarzoma a birnin Lagos.

Mujallar ta "Time" ta ce a karshen wannan ganawa, inda aka roki wakilan da su rage yada munanan labarai da suka shafi Nijeriya, an mikawa kowane wakili kunshin takardun bayanai, ciki har da wani ambulon mai dauke da kudi dalar Amurka 400.

Kamfanin dillancin labaran Reuta ya ce wakilinsa ya mayar da wannan kudi da aka ba shi, kamar yadda wasu wakilan da dama suka yi.

Ministan yada labarai na Nijeriya, Jerry Gana, ya musanta cewa wannan kudi cin hanci ne, yana mai cewa an bai wa 'yan jaridan ne domin su biya kudin sufuri da na hotel.

Ministan shari'a na Nijeriya, Kanu Agabi, ya ce zargin bada cin hanci da mujallar "Time" ta buga ba ya da tushe. Yayi kashedin cewa a nan gaba, 'yan sandan Nijeriya zasu binciki duk wani rahoton da aka hakkake cewa na karya ne, a kuma hukumta dan jaridar da ya rubuta.

XS
SM
MD
LG