Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Da Yarima Abdullahi Zasu Gana Yau Alhamis A Texas - 2002-04-25


Shugaba George Bush da Yariman Sa'udiyya mai jiran gado Abdullahi, za su gana a wani lokaci a yau alhamis a gonar shugaban ta kiwon dabbobi dake Jihar Texas, inda ake kyautata zato zasu fi maida hankali akan yadda za'a yi a samu ci gaban shirin da Yariman Sa'udiyyar ya bada domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shirin dai yayi tanadin cewa Isra'ila ta janye daga illahirin yankunan da ta kame a lokacin yakin gabas ta Tsakiya a shekarar 1967, kambacin hakan, su kuwa kasashen Larabawa su yi cikakkiyar yarda da matsayin kasar ta Isra'ila.

Ana kyautata zato Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya, zai caccaki kokarin da Amurka ta ke yi na samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, zai kuma bayyana shi wannan kokari a zama mai marawa bangare guda kawai, kuma mai nuna fifiko ga Isra'ila.

A jiya laraba a birnin Houston, Yarima Abdullahi ya gana da Dick Cheney, mataimakin shugaban Amurka, da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka. A jiyan an sa ran ganin ganawar Yarima Abdullahi da Dick Cheney ta fi maida hankali kan batutuwan kasuwanci da na tsaro.

Haka nan kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai halarci ganawar da Yarima Abdullahi da shugaba Bush zasu yi a wani lokaci a yau alhamis.

Mr.Powell ya ce zai nemi sanin inda za'a yi da kudaden nan fiye da dalar Amurka miliyan dari da kasar Sa'udiyya ta tara kwanakin baya da sunan taimaka wa Falasdinawa. A jiya laraba, Mr.Powell ya shaidawa wani kwamitin majalisar dattijan Amurka cewa, gwamnatin Amurka ta ga alamun cewa daga cikin wadannan kudade wasu zasu ne ga kungiyar Hamas ta 'yan gwagwarmayar kwatar 'yancin kan Falasdinawa--ya bayyana yiwuwar hakan a zama wani al'amari mai tada hankali.

XS
SM
MD
LG