Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Isra'ila Da Wasu Jami'an MDD Suna Tattaunawa A New York... - 2002-04-26


Wakilan Isra'ila sun gana da jami'an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, jiya alhamis a birnin New York, inda suke kokarin ganin an sake fasalin tawagar majalisar wadda zata binciki abubuwan da suka wakana a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun yi kisan gillar fararen hula, abinda Isra'ila ta ce ba haka ne ba.

An dage tattaunawar da jami'an sassan biyu suka yi bayan sa'o'i biyu da rabi, amma ana sa ran zasu ci gaba a yau Jumma'a.

A bisa bukatar da Isra'ila tayi, MDD ta kara mashawartan soja biyu a cikin tawagar. Har ila yau Isra'ila tana son jami'an tawagar su binciki abinda ta ce wai ayyukan ta'addanci ne da Falasdinawa ke gudanarwa a cikin sansanin.

Kwamitin sulhun MDD ya ce duk da wannan tattaunawa dake gudana, tawagar zata isa yankin Gabas ta Tsakiya a karshen makon nan.

A halin yanzu kuma, Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, sun ki karbar kayayyakin agajin da Amurka ta tura musu, domin su nuna bacin ran agajin makaman yakin da Amurka take bai wa Isra'ila.

Jami'an Falasdinawa a Jenin, sun ce mazauna sansanin sun ki sauke kayan abinci, tantuna da kayan wasan yara wadanda suka isa can cikin motocin dakon kaya daga hukumar tallafawa kasashen waje ta Amurka.

Wani kakaki a sansanin ya ce mazauna wannan sansani ba zasu karbi kayan agaji daga Amurka ba, a saboda sojojin Isra'ila sun yi amfani da makaman Amurka wajen rushe musu gidajen kwanansu.

Falasdinawan suna zargin Isra'ila da laifin yin kashe-kashen gilla cikin wannan sansani dake yankin Yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG