Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Yarima Abdullahi Sun Tattauna Batun Gabas Ta Tsakiya - 2002-04-26


Shugaba Bush ya ce Amurka da Sa'udiyya suna kwadayin ganin an samu kasashe biyu, Isra'ila da Falasdinu, suna zaune lami lafiya cikin tsaro da junansu.

Mr. Bush yayi wannan furucin a bayan ganawar sa'o'i biyar da yayi a gonar kiwon dabbobinsa dake garin Crawford, a Jihar Texas, tare da Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya.

Shugaba Bush yayi kira ga Isra'ila da ta warware cirko-cirkon da ake yi a Bethlehem da Ramallah cikin lumana, ta kuma janye baki daya daga yankunan Falasdinawa na yankin Yammacin kogin Jordan. Ya kuma ce tilas su ma shugabannin Falasdinawa su kara tashi tsaye domin kawo karshen ta'addanci.

Yarima Abdullahi ya shaidawa Mr. Bush cewar ya kamata Amurka ta kara matsin lamba kan Isra'ila domin ta kawo karshen farmakin da take kaiwa a yankin Yammacin kogin Jordan, ta kuma sako shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat daga talalar da tayi masa.

XS
SM
MD
LG