Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Madagascar Ya Ce Allambaram, Ba Zai Yarda Da Sakamakon... - 2002-04-29


A wani matakin da ya kara rura wutar rikicin siyasa a kasar Madagascar, shugaba Didier Ratsiraka ya ce ba zai yarda da sakamakon sake kidaya kuri'un da za a bayyana yau litinin ba.

Furucin da Mr. Ratsiraka yayi jiya lahadi, ya biyo bayan barazanar da magoya bayansa suka yi cewa su ma ba zasu yarda da adadin da za a bayyana na sake kidaya kuri'un ba.

A makon jiya a kasar Senegal, shugaban tare da madugun hamayya, Marc Ravalomanana, sun yarda zasu warware rikicin da suke yi ta hanyar kiran da a sake kidaya kuri'un.

Mr. Ratsiraka ya bayyana sake kidaya kuri'un da Babbar Kotun Tsarin Mulki ta kasar ke yi da cewa ya "sabawa doka," ya kuma yi kiran da a gudanar da kuri'ar raba-gardama. Dukkan mutanen biyu suna ikirarin lashe kujerar shugabancin kasar a bayan zaben da aka yi a watan Disamba.

Madagascar ta fada cikin tarzomar siyasa tun lokacin da Mr. Ravalomanana, wanda shine magajin garin Antananarivo, babban birnin kasar, ya ayyana kansa a zaman shugaban kasa cikin watan Fabrairu. Yayi zargin cewa an tabka magudi, ya kuma ki yarda da umurnin kotu na gudanar da zaben fitar da gwani.

An kashe mutane akalla 32 a tashe-tashen hankula masu alaka da wannan rikici.

XS
SM
MD
LG