Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Sa'udiyya Ya Ce Ba Zasu Goyi Bayan Daukar Matakan Soja Ba... - 2002-04-29


Ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Sa'ud al-Faisal, ya ce kasarsa tana yin adawa da matakan soja a kan Iraqi, muddin shugaba Saddam Hussein ya kyale sufetocin makamai na MDD suka koma cikin kasar.

Sa'ud al-Faisal ya ce babu wata bukatar daukar matakan soja idan har akwai sufetocin makamai na MDD cikin Iraqi wadanda zasu kawar da duk wata damuwar da Amurka take da ita game da makaman kare-dangin da Iraqi ta mallaka. Ya ce wani dalili kuma na rashin yarda da kai wa Iraqi farmaki, shi ne alkawarin da Iraqin tayi cewa har abada ba zata sake kai hari kan kasar Kuwaiti ba.

Ministan harkokin wajen na Sa'udiyya bai ce ko kasarsa zata kyale Amurka ta yi amfani da sansanoninta na sama wajen daukar duk wani matakin soja kan Iraqi ba.

Ya kuma sake jaddada bukatar girka rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa a yankunan Falasdinawa, yana mai cewa 'yan kallo kawai ba zasu iya warware wannan rikicin ba, ganin yadda tashin hankali yayi tsanani.

XS
SM
MD
LG