Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Mali Suna Zaman Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da Suka Yi - 2002-04-30


Masu jefa kuri'a na kasar Mali suna zaman jiran sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar lahadi, inda ake kyautata zaton sai an gudanar da zagaye na biyu.

'Yan takara har 24 suka yi takara a wannan zabe na maye gurbin shugaba Alpha Oumar Konare, wanda tsarin mulki ya hanawa tsayawa takara a wa'adi na uku na karin shekaru 5.

Masu fashin baki sun ce an gudanar da wannan zabe sumul, koda yake an samu 'yan matsaloli kalilan a wasu rumfunan zabe. A wasu wuraren, an fuskanci karancin takardun kuri'u, a wasu wuraren kuma, masu jefa kuri'a sun tafi rumfunan ba tare da katunansu na rajista ba.

Ganin cewar yana da wuya a samu dan takara guda da zai lashe rabin dukkan kuri'un da aka jefa, tuni har an tsayar da ranar 12 ga watan Mayu ta zamo ranar gudanar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani.

Wadanda aka yi imanin cewa sune ke kan gaba a wannan zabe sun hada da tsohon firayim minista Ibrahim Boubacar Keita, da tsohon ministan kare muhalli Soumaila Cisse da kuma tsohon janar na soja, Ahmadou Toumani Toure.

Daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta a game da wannan zabe ita ce kasar Mali tana daya daga cikin kasashen da suka fi fadin kasa a nahiyar Afirka, inda take da fadin murabba'in kilomita miliyan daya da wani abu.

Jami'an zabe suka ce ana daukar lokaci wajen tattaro akwatunan zabe da kuri'u daga yankunan dake cikin lungu.

XS
SM
MD
LG