Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ravalomanana Yayi Kiran Da A Samu hadin Kan Kasa A Madagascar - 2002-04-30


Madugun adawar kasar Madagascar, Marc Ravalomanana, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ake gardama a kai, yayi kiran da a samu hadin kan kasa, a bayan da shugaba mai barin gado, Didier Ratsiraka, ya ce ba zai yarda da sakamakon da aka bayyana bayan sake kidaya kuri'un ba.

Mr. Ravalomanana ya shaidawa taron manema labarai jiya litinin a Antananarivo, babban birnin kasar, cewar yana kira ga Mr. Ratsiraka da ya amince da wannan sakamako, ya kuma dafa wajen hada kan al'ummar kasar.

Har ila yau a jiya litinin ne Babbar Kotun Tsarin Mulki ta Madagascar ta ayyana Mr. Ravalomanana a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Disamba da ake gardama a kai, bayan da aka sake kidaya kuri'un bisa umurnin kotun kolin kasar.

Kotun ta ce Mr. Ravalomanana ya lashe kashi 51 daga cikin 100 na dukkan kuri'un da aka jefa, yayin da Mr. Ratsiraka ya samu kashi 36 daga cikin 100 kawai na kuri'un.

Mr. Ratsiraka ya ki yarda da wannan sakamako, yana mai bayyana sake kidaya kuri'un da aka yi a zaman abinda ya sabawa doka. Ya bukaci da a gudanar da kuri'ar raba-gardama a kasar kan wannan kujera ta shugaba.

Amurka ta ce tana nazarin wannan hukumci da kotun ta Madagascar ta cimma.

Madagascar ta fada cikin rigimar siyasa tun lokacin da Mr. Ravalomanana ya ki yarda da sakamakon zaben na watan Disamba, yana mai zargin cewa an yi magudi wajen kidaya kuri'un.

XS
SM
MD
LG