Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Suna Ci Gaba Da Mamaye Unguwannin Falasdinawa A Hebron... - 2002-04-30


Sojojin Isra'ila suna ci gaba da mamaye unguwannin Falasdinawa na garin Hebron, a bayan da suka kai farmaki ciki jiya litinin, suka kashe Falasdinawa 9, suka kama wasu 17.

Isra'ila ta ce wannan mamaye nata na wucin gadi ne, wanda kuma ta kai da nufin "murkushe cibiyoyin 'yan ta'adda na Hebron" a fadinta.

Wannan farmaki da Isra'ila ta kai ya biyo bayan wani harin da Falasdinawa suka kai cikin wata unguwar share-ka-zauna ta yahudawa a ranar asabar, inda suka kashe 'yan Isra'ila 4.

A halin da ake ciki, sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce watakila nan bada jimawa ba za a cimma yarjejeniyar kawo karshen dambarwar da ake yi a majami'ar "Nativity" dake birnin Bethlehem. Amma jami'an shawarwari na Falasdinawa sun ce an dakatar da tattaunawa har sai Isra'ila ta kyale an kai abinci ga mutanen dake cikin wannan coci.

Falasdinawa kimanin 200, cikinsu har da 'yan bindiga kimanin 30, sun shafe kwanaki 28 suna boye cikin cocin.

XS
SM
MD
LG