Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Ci gaba Da Tsara Shirin Kawar Da Talalar Da Isra'ila Tayi Wa Yasser Arafat - 2002-04-30


Jami'an Amurka da Britaniya da na Falasdinawa zasu sake ganawa a yau talata domin tsara dalla-dallar shirin kawo karshen kofar-ragon da Isra'ila tayi wa shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat.

Wani jami'in Falasdinawa ya bayyana tattaunawar da aka yi jiya litinin a Ramallah a zaman mai amfani. Tun watan Disamba Isra'ila ta yi talala wa Yasser Arafat a hedkwatarsa dake Ramallah.

A karkashin wannan shirin da Amurka ta tsara, kuma dukkan sassan biyu suka yarda da shi, Isra'ila zata ba da Malam Arafat 'yancinsa na walwala da zarar an dauki 'yan kishin Falasdinu shida da Isra'ilar take nema, daga Ramallah zuwa wani gidan kurkukun Falasdinawa dake garin Jericho.

Masu gadin Amurka da na Britaniya sune zasu kula da yadda ake tsare da Falasdinawan. Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce yana sa ran za a tsara dalla-dallar wannan shiri nan bada jimawa ba.

XS
SM
MD
LG