Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Yi Kiran Da A Kakaba Wa Isra'ila Takunkumi - 2002-05-01


Jami'an Falasdinawa sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da ta kakaba wa Isra'ila takunkumi, sai fa idan gwamnatin Isra'ilar ta bayar da hadin kai ga wata tawaga da majalisar ta tura sansanin 'yan hijira na Jenin, domin ganin kwakwaf.

Falasdinawa sun ce, kememen da Isra'ila ta yi, ta ki yin aiki da wannan ayari na MDD, yana nuna cewa dakarun Isra'ilar sun aikata laifuffukan yaki a wannan sansani. Da kwakkwaran lafazi, Isra'ila ta musanta wannan korafi na Falasdinawa mai cewa sojojinta sun karkashe jama'a a sansanin na Jenin, yayin farmakin da suka kai yankin Yammacin kogin Jordan cikin watan jiya.

Tun farko a jiya talata, wani babban jamiin MDD ya ce babban magatakardar majalisar, Kofi Annan, yana tunanin yin watsi da wannan aiki na tura tawagar binciken zuwa Jenin, saboda Isra'ila ta ki ba da hadin kai.

Gwamnatin Isra'ila dai, ta ce, ita ba za ta yi aiki da wannan tawaga ba, har sai an biya bukatun da ta gitta, gameda fasali, da kuma irin aikin da ayarin na MDD zai yi.

XS
SM
MD
LG