Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Falasdinawa Uku A Zirin Gaza, Ciki Har Da 'Yar Jaririya - 2002-05-01


Falasdinawa sun ce an kashe mutane, ciki har da wata jaririya mai shekaru biyu da haihuwa, a gwabzawar da aka yi tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa 'yan bindiga a kudancin zirin Gaza, kusa da bakin iyaka da Misra.

Suka ce an kashe wannan jaririya da mutum guda a lokacin da wata tankar yaki ta Isra'ila ta yi harbi kan gidansu yau laraba da asuba a Rafah.

Falasdinawa suka ce jim kadan a bayan wannan, tankokin yakin Isra'ila sun shiga cikin garin, inda aka goce da harbe-harbe, har aka kashe wani Bafalasdine.

Rundunar sojojin Isra'ila ba ta ce uffan ba game da wannan lamarin. Amma kamfanin dillancin labaran Reuta, ya ambaci wata majiyar sojan Isra'ila tana fadin cewa tankar yaki guda tayi harbi sau daya kan gungun "wasu 'yan ta'adda" da suka tayar da bam a gefen hanya, kusa da wata mota mai sulke ta Isra'ila dake sintiri a bakin iyaka.

Tun da fari, rundunar sojojin ta ce ta janye dukkan sojojinta daga yankunan da Falasdinawa suke mulkinsu a cikin birnin Hebron, a Yammacin kogin Jordan. Rundunar sojan ta bani Isra'ila ta ce a lokacin wannan farmaki na kwanaki biyu, ta kama mutane 150 wadanda ake zaton suna gudanar da ayyukan ta'addanci, an kuma kwace bindigogi da nakiyoyi.

Har ila yau, an ce janyewar ta hada da sojojin da suka yi kawanya wa 'yan kishin Falasdinu su 20 a wani asibitin dake birnin Hebron.

A birnin Bethlehem kuma, Falasdinawa 26 sun bar majami'ar "Nativity." Wannan shine adadi mafi yawa da suka bar majami'ar tun lokacin da sojojin Isra'ila suka kewaye wurin a ranar 2 ga watan Afrilu. Rundunar sojojin Isra'ila ta ce rabin wadanda aka sako jami'an tsaron Falasdinawa ne, sauran kuma fararen hula.

XS
SM
MD
LG