Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar MDD Tana Son A Kwashe Dukkan Sojoji Daga Birnin Kisangani - 2002-05-02


Jagoran tawagar da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya tura zuwa Kwango-Kinshasa yayi kira ga dakarun sassan dake yakar juna da su fice daga Kisangani - birni na biyu wajen girma a kasar.

A bayan da ya ziyarci birnin jiya laraba, jakadan Faransa a MDD, Jean-David Levitte, ya shaidawa 'yan jarida cewa Kwamitin Sulhu zai bada muhimmanci sosai ga kokarin kawar da dukkan sojoji daga cikin birnin.

Mr. Levitte, wanda ke jagorancin wannan tawaga mai wakilai 15, ya ce birnin na Kisangani ya zamo abinda ya kira "alama ta bakar wahala."

Daruruwan fararen hula 'yan kasar ta Kwango-Kinshasa sun mutu, yayin da sojojin Uganda da Rwanda suka yi ta gwabzawa da juna don neman mallakin wannan birni dake bakin kogi.

Tawagar ta MDD zata yi rangadin kasashen Afirka takwas a wani kokari na karfafa shirin wanzar da zaman lafiya a Kwango Kinshasa.

A ranar talata, tawagar ta gana da shugaba Joseph Kabila na Kwango-Kinshasa, wanda ya bayyana aniyarsa ta kafa gwamnatin rikon-kwarya tare da 'yan tawaye.

Yakin basasar da aka fara a shekarar 1998 a Kwango-Kinshasa, ya hada gwamnatin kasar da 'yan tawayen dake samun goyon bayan sojojin kasashen Uganda da Rwanda. Su ma kasashen Angola, Namibiya da Zimbabwe sun tura sojojinsu domin dafawa dakarun gwamnati.

XS
SM
MD
LG