Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Yayi Sanadin Mutuwar Wasu Mutane A Kenya - 2002-05-02


Ana fargabar cewa mutane akalla goma sun mutu a Kenya, bayan da laka ta kwararo ta rufe gidaje guda takwas lokacin da ake sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin gabashin kasar.

Jaridun kasar Kenya, sun ambaci wani jami'in 'yan sanda, Ezekiel Waitage, yana fada jiya laraba cewa an ciro mutane biyu da ransu daga cikin lakar, an kuma gano gawarwaki guda shida. Ya ce har yanzu ba a san inda mutane hudu suke ba.

An fara ruwan saman tare da kwararar laka tun ranar talata da safe a wannan kauye mai suna Giumpu, a gundumar Meru.

Da yawa daga cikin yankunan kasar ta Kenya sun fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokuta da dama cikin 'yan kwanakin nan. Ma'aikatar kula da yanayin samaniya ta Kenya, ta ce an samu wannan sauyin yanayi ne a saboda yadda tekun Indiya yake kara yin dumi.

XS
SM
MD
LG