Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Rushe Tawagar Binciken Abubuwan Da Suka Faru A Jenin... - 2002-05-02


Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce zai rushe tawagar da ya kafa domin ta binciki abubuwan da suka faru a sansanin Falasdinawa 'yan gudun hijira na Jenin.

A cikin wasikar da ya aikewa da Kwamitin Sulhun majalisar, Mr. Annan ya ce a yau alhamis zai rushe wannan tawaga da ya kafa.

Isra'ila ta ki yarda ta yi aiki tare da tawagar tana mai cewa ba ta yarda da wakilan tawagar da kuma irin ayyukan da zasu gudanar ba. Tsohon shugaban kasar Finland, Martti Ahtisaari, shine aka nada jagoran wannan tawaga.

Jami'an Amurka sun ce sun ji takaicin wargajewar wannan tawaga.

Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun karkashe fararen hula cikin ruwan sanyi a lokacin da suka kai farmaki sansanin a watan da ya shige. Isra'ila ta musanta da kakkausar harshe.

Mr. Annan ya ce a kowace rana, yanayi da lamurra suna canjawa a sansanin na Jenin, suna kara wahalar iya tantance zahirin abubuwan da suka faru a can.

A wani gefen kuma, wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta likitoci ta nan Amurka, ta ce fiye da sulusin Falasdinawan da aka kashe a farmakin da Isra'ila ta kai Jenin, da kuma rabin wadanda suka ji rauni, duk ad alamun fararen hula ne.

Kungiyar mai suna "Physicians for Human Rights" ta ce binciken farkon da ta gudanar a sansanin cikin makon jiya, ya nuna cewa akasarin fararen hular da aka kashe, yara ne 'yan kasa ad shekara 15, da mata, da kuma tsoffi 'yan fiye da shekaru 50 da haihuwa.

Kungiyar ta ce akwai bukatar gaggawa ta gudanar da cikakken bincike tsakani da Allah na abubuwan da suka faru cikin sansanin.

Kungiyar ta ce ta tabbatar ad mutuwar Falasdinawa 45 cikin sansanin, amma kuma ta ce ainihin yawan wadanda suka mutu zai iya zarce haka.

Ta ce mutane akalla 100 sun ji rauni, kuma da yawa daga cikinsu sun shafe fiye da kwanaki uku ko hudu kafin a kai su jinya, duk da cewa a bayyane yake rauninsu na iya zamowa ajalinsu.

XS
SM
MD
LG