Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Malam Yasser Arafat - 2002-05-02


Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya samu 'yancin sakewa ya yawata yadda ya ga dama, bayan janyewar sojojin Isra'ila daga Ramallah da jijjifin yau alhamis.

Watanni biyar sojojin Isra'ila suka yi suna kange da Malam Yasser Arafat, da farko iyakacinsa birnin Ramallah kawai, sannan kuma kawai sai dai ya tsaya cikin harabar hedkwatarsa.

Sojojin Isra'ilar sun fara janyewa ne bayan da aka kai wasu Falasdinawa 6 mayakan kwatar 'yanci wani gidan kason Falasdinawa dake Jericho a karkashin wata jituwar da aka cimma da taimakon shiga tsakanin Amurka. Jami'an tsaron Amurka da na Birtaniya ne zasu yi gadinsu a gidan kason.

Jami'an Falasdinawa sun ce yanzu dai malam Yasser Arafat zai ci gaba da zama a hedkwatarsa da ruwan rikici ya ciwo. Firayim ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya shaidawa wani gidan telebijin na Amurka cewa malam Yasser Arafat na da 'yancin zuwa inda ya ga dama a duniya, amma ya ce watakila ba za'a sake barin shi ya koma kasar ba idan aka kai wani harin ta'addanci a lokacin da ba ya kasar.

Lokacin da yayi furucinsa na farko bayan janyewar sojojin Isra'ilar, malam Yasser Arafat, cikin fushi, yayi tur da Allah waddai da matakan da Isra'ila ta dauka a majami'ar nan ta Bethlehem wato "The Church of the Nativity" ko kuma "La Basilique de la Nativite," inda sojojin Isra'ila da Falasdinawa 'yan bindiga suka fafata wani kazamin fada a yau alhamis.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kewaye Falasdinawa su kimanin 200, daga cikinsu wasu dauke da makamai, wadanda ke ci gaba da fakewa a wurin mai tsarki ga Kiristoci. Shugaban Falasdinawan ya bayyana matakan da Isra'ilar ta dauka a zama "mugun aikin keta", sannan kuma yayi tambayar cewa ta yaya kasashen duniya suna ji suna gani zasu ja bakinsu su yi shiru game da abubuwan dake faruwa a majami'ar.

Kowane bangare na zargin dan'uwansa da fara fadan na yau alhamis. Wata gobara ta barke a kusa da majami'ar, amma nan da nan cikin gaggawa aka shawo kanta.

XS
SM
MD
LG