Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Hotunan Duniyoyi Da Tabaron Hubble Ya Dauko - 2002-05-02


Tabaron hangen nesa na Hubble, wanda aka girka a sararin samaniya, wanda kuma 'yan sama jannatin Amurka suka makala masa sabon madubi kwanakin baya, ya dauko wasu hotunan da Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta bayyana a zaman hoton falaki mafi mamaki da aka taba gani.

Masana taurari da masu binciken sararin samaniya a nan Amurka, wadanda ke cike da murna, sun bayyana sabbin hotunan, wadanda sabon madubin nan mai suna "Advanced Camera for Surveys" ya dauko su, wadanda kyaunsu da fitowarsu ya ninka duk wani hoto makamanci da aka taba gani sau goma.

Masana kimiyyar suka ce sun yi mamaki matuka da ganin wadannan hotuna.

Wadannan hotuna da aka bayyana sun hada har da hoton wani falaki mai suna "Tadpole", ko Dandala-Kwadi a Hausance(saboda siffarsa), mai nisan shekaru miliyan 420 na tafiyar haske daga wannan falaki namu.

Sauran hotunan sun hada da na karo tsakanin wasu falaki guda biyu, wadanda masana taurari suka sanyawa suna "Mice" ko kuma beraye, a saboda za a gansu kamar suna kewaye juna sannu a hankali.

Masana kimiyya suka ce karon da aka yi tsakanin wannan falaki mai suna "Mice" yana iya nuna irin makomar da zata shafi wannan falaki namu mai suna "Milky Way" nan gaba. Na'urorin hasashe sun nuna cewar nan da wasu dubban miliyoyin shekaru zai yi karo da falakin dake kusa da mu, mai suna "Andromeda."

XS
SM
MD
LG