Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Tara Sun Sheka Barzahu A Lokacin Da Nakiya Ta Tashi A Sudan - 2002-05-03


An bada rahoton cewa fararen hula su akalla 9 sun mutu, wasu guda 15 kuma sun ji rauni, a lokacin da wata nakiya ta tashi a yankin kudancin Sudan.

Kamfanin dillancin labaran Sudan, "SUNA", ya ambaci wata sanarwar gwamnati tana zargin 'yan tawayen kungiyar "SPLA" da laifin dana wannan nakiya.

Kungiyar 'yan tawayen ba ta maida martani kan wannan rahoto ba.

Kamfanin dillancin labaran ya ce wannan nakiya ta tashi a kusa da Wau, gari mafi girma a Jihar Bahr-el-Ghazal dake kudancin kasar. Rahoton ya ce nakiyar ta tashi a karkashin waata motar dake dauke da jami'an lardi da wasu jami'an dake kan hanyar zuwa wata cibiyar rarraba abinci. Ya ce akwai wani kwamishinan lardi cikin wadanda aka kashe.

Kungiyar SPLA ta fara yakar gwamnatin Sudan tun shekarar 1983. Mutane har miliyan biyu suka mutu a wannan rikicin, akasarinsu a saboda bala'in yunwar da yakin ya haddasa.

XS
SM
MD
LG