Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lahadin Nan Za A Ci Gaba Da Aikin Ceto A Kano... - 2002-05-05


Ana sa ran ma'aikatan agaji a birnin Kano dake yankin arewacin Nijeriya, zasu ci gaba da aikin nemo gawarwakin mutanen da suka mutu, a lokacin da wani jirgin sama yayi hadari jiya asabar.

Shaidu sun ce wannan jirgin sama, wanda aka yi imanin cewa yana dauke da mutane akalla 75, ya abka kan gidaje da masallatai a wata unguwar dake shake da mutane, ya kuma kama da wuta, duk a lokacin da yake kokarin tashi asabar din nan daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Jami'an Nijeriya sun ce har yanzu ba a san musabbabin hadarin wannan jirgi ba. Haka kuma babu tabbas ko akwai wani ko wasu da suka kubuta da rayukansu daga wannan hadari. Wani rahoton ya ambaci shaidu na fadin cewa mutane biyu sun tsira da rayukansu.

Ma'aikatan agaji a wurin da wannan hadari ya faru sun ce mutane akalla 40 sun mutu a kasa, watau wadanda jirgin ya abka kansu.

An ga mazauna wannan unguwa a cikin tsananin damuwa da tashin hankali suna yawo a gigice suna neman 'yan'uwansu, wadanda watakila suna karkashin gine-ginen da suka rushe a kusa da inda jirgin ya fadi.

An ambaci hukumomin Nijeriya suna fadin cewa wannan jirgi samfurin 1-11-500 kirar kamfanin "British Aerospace" na Ingila, ya taso ne tun asali daga Lagos, ya biya ta garin Jos.

Wani rahoton ya ambaci jami'an zirga-Zirgar jiragen sama suna fadin cewa jirgin yana dauke ad wasu manyan kusoshin gwamnatin Nijeriya, cikinsu har da wani minista, wadanda suka halarci wani biki na kaddamar da littafi a Kano.

Jirgin na wani kamfanin safarar jiragen saman Nijeriya mai zaman kansa ne da ake kira EAS Airlines, daya daga cikin kamfanoni masu yawa dake aikin safarar jiragen sama a cikin gida a Nijeriya.

Kungiyar Kula da Hadarurrukan Jiragen Sama a Duniya mai hedkwata a kasar Holland, ko Netherlands, ta ce kama daga shekarar 1963, irin wannan samfurin jirgi yayi hadari sau 28.

XS
SM
MD
LG