Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Makoki A Nijeriya... - 2002-05-05


Jami'an kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya sun ce ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin mutane 148 daga inda wani jirgin sama ya fadi a birnin Kano, dake arewacin kasar.

Wani kakakin kungiyar agajin, ya ce yawam wadanda suka mutu yana iya karuwa, yayin da ma'aikatan ceto suke ci gaba da tono gine-ginen da wannan jirgi ya rusa lokacin wannan mummunan hadari na ranar asabar. Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ambaci wata sanarwa ta kungiyar Red Cross ta Nijeriya, tana fadin cewa jirgin ya lalata gidaje fiye da 30, ya sa daruruwan mutane suka rasa matsuguni.

Jami'ai sun ce mutum daya daga cikin ma'aikatan jirgin, da kuma fasinjoji uku sun kubuta da rayukansu a lokacin da wannan jirgin sama mai injuna biyu, kirar kasar Ingila, ya fadi.

Hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Nijeriya, sun ce akwai fasinjoji 69 da ma'aikata 7 cikin wannan jirgin saman kamfanin EAS dake kokarin tashi zuwa Lagos.

Shaidu sun ce sun ga wuta na ci bal-bal daga wannan jirgi a daidai lokacin da zai fada kan wata unguwar dake kusa da filin jirgin na Kano, jim kadan a bayan tashinsa.

Ba a san dalilin faduwar wannan jirgi ba.

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya yayi alkawarin za a gudanar da cikakken bincike na wannan lamari. Shugaban na Nijeriya ya katse ziyarar ad yake yi a wasu kasashen yankin kudancin Afirka, ya kuma ayyana zaman makoki na kwanaki biyu a duk fadin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG