Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Sun Yi Kusan Cimma Yarjejeniyar Kawo Karshen Tankiyar Bethlehem - 2002-05-06


Jami'an Isra'ila da na Falasdinawa sun ce mashawarta sun yi kusan cimma yarjejeniyar da zata kawo karshen kawanya da farmakin da Isra'ila take yi wa majami'ar "Nativity" a Bethlehem.

Tun da fari kuwa, jami'an Falasdinawa sun ce sassan sun cimma yarjejeniya, amma jami'an tsaro na Isra'ila sun musanta haka.

An ce sassan biyu sun kasa daidaitawa a kan ko 'yan kishin Falasdinu nawa ne dake cikin majami'ar zasu tafi hijirar dole, da kuma inda za su tafi din.

Tun fari, jami'an Falasdinawa sun ce za a tura 'yan kishin Falasdinu 6 zuwa hijira a kasar Italiya, wasu guda 30 kuma za a kai su Zirin Gaza, inda za a yi musu shari'a a kotunan Falasdinawa. Duk sauran wadanda ke cikin majami'ar kuma za a kyale su, suyi tafiyarsu.

Isra'ila ta killace majami'ar a ranar biyu ga watan Afrilu, a bayan da Falasdinawa su fiye da 200, wasu dauke da makamai, suka nemi mafaka cikin majami'ar a lokacin da sojojin Isra'ila suka kai farmaki cikin garin na Bethlehem.

A jiya lahadi, jami'an Falasdinawa sun mika wa Isra'ila sunayen mutane 123 wadanda har yanzu suke cikin majami'ar, wadda aka gina a inda mabiya addinin kirista suka yi imanin cewa an haifi Annabi Isa Alahis Salam.

XS
SM
MD
LG