Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Burma Sun Sako Aung San Suu Kyi - 2002-05-06


Gwamnatin mulkin soja ta Burma ta saki babbar jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi, bayan daurin talalar watanni 19 da aka yi mata cikin gidanta.

Wani kakakin gwamnatin ya fada a yau litinin, cewar an dage dukkan kangin zirga-zirga ko ayyukan da aka sanyawa wannan mace, wadda ta taba lashe lambar yabon Nobel ta neman a zauna lafiya.

Tun cikin watan Satumbar shekarar 2000 aka tsare 'yar rajin dimokuradiyyar a cikin gidanta, a bayan da ta nemi yin watsi da haramcin da gwamnati ta kafa mata na tafiya wani wuri a wajen babban birnin kasar, Rangoon.

An yi kwana da kwanaki ana sa ran ganin an sako ta, a bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani a kokarin warware rikicin siyasar da aka shafe shekaru 12 ana yi a kasar ta Burma.

Ita dai jam'iyyar "National League for Democracy" ta Aung San Suu Kyi, ta lashe zaben da aka yi a kasar Burma a 1990 da gagarumin rinjaye, amma sai sojoji suka ki yarda su mika mata mulki.

XS
SM
MD
LG