Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnatin Colombia Suna Kokarin Kwato Kauyuka... - 2002-05-06


Dubban sojojin gwamnatin Colombia suna kokarin sake kwato wasu kauyuka tare da ceto mutane a kungurmin dajin arewa maso yammacin kasar, a bayan da mutane fiye da 100 suka mutu a kazamin fada tsakanin 'yan tawaye masu ra'ayin gurguzu da sojojin sa kai masu ra'ayin 'yan mazan jiya, cikin 'yan kwanakin da suka shige.

Hukumomin Colombia sun ce an kashe mutane akalla 107, cikinsu har da yara kimanin 40, a wasu kauyuikan dake cikin kurmi a Jihar Choco, inda 'yan tawayen kungiyar FARC da sojojin sa kai na Hadaddiyar Rundunar Kare Kai Ta Colombia suke gwabzawa domin jaddada ikonsu a wannan wuri.

Jihar Choco tana daya daga cikin wadanda suka fi talauci a Colombia, kana tana daya daga cikin wuraren da aka yi fama da tashin hankali. Jami'ai suka ce ana yin wannan fada a yankin ne domin neman mallakin hanyoyin safarar muggan kwayoyi masu matukar muhimmanci.

Hukumomi suka ce da yawa daga cikin wadanda suka mutu, sun hallaka ne a lokacin da 'yan tawayen FARC suka jefa kwanson nakiya hadin gida a cikin wata majami'a, inda mutane da yawa suka nemi mafaka.

XS
SM
MD
LG