Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Zauren Shawarwarin MDD Zai Tattauna Kudurin Yin Tur Da Bani Isra'ila... - 2002-05-07


A yau talata, Babban Zauren Shawarwari na MDD zai nazarci wani kudurin dake yin Allah wadarai da Bani Isra'ila, a saboda muggan ayyukan da ake zargin ta aikata lokacin farmakin da ta kai yankin Yammacin kogin Jordan kwanakin baya.

Kasashen Larabawa sune suka bukaci da a yi wannan zama, a bayan da Kwamitin Sulhun majalisar ya kara tura tawagar bincike zuwa cikin sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da Isra'ila ta maida kango. Isra'ila ta ki yarda tayi aiki tare da tawagar, tana mai korafin manufofi da kuma irin wakilan tawagar.

Babban Zauren shawarwari na MDD ya sha zartas da kudurorin yin Allah wadarai da Isra'ila cikin 'yan shekarun nan, kuma ana kyautata zaton wannan ma za a zartas da shi.

Sai dai kuma kudurin babban zauren ba ya da tasiri kamar an Kwamitin Sulhu, wanda shi ya zamo tilas kasashe membobi suyi aiki da shi.

A can wani gefen kuma, Isra'ila tayi zargin cewa kasar Sa'udiyya tana tura kudade ga kungiyoyi da 'yan kishin Falasdinawa masu kai hare-hare kan Isra'ila.

Rahoton da jami'an Isra'ila suka bayar a nan Washington yayi zargin cewa Sa'udiyya ta tura "kudi mai yawan gaske" ga iyalan 'yan kunar-bakin-wake da kuma kungiyar Hamas ta 'yan kishin Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambaci wata sanarwa ta gwamnatin Sa'udiyya tana bayyana wannan zargi na Bani Isra'ila a zaman abin kunya, kuma mai neman juya hannun agogo baya.

Sanarwar ta ce ta'addanci ya sabawa addini da al'adun Sa'udiyya, kuma Isra'ila ta yi wannan zargin ne da nufin kawar da hankalin jama'a daga kokarin da Sa'udiyya take yi na wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG