Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Kara Wa'adin Aiki Da Takunkumin Da Ta Kakaba Wa Liberiya - 2002-05-07


Kwamitin Sulhun MDD ya jefa kuri'ar kara wa'adin yin aiki da takunkumin da aka kafa kan kasar Liberiya da shekara guda.

Dukkan wakilai 15 na Kwamitin Sulhu sun jefa kuri'ar amincewa da wannan kuduri litinin din nan. Kwamitin ya yanke shawarar cewa har yanzu gwamnatin Liberiya ba ta yi aiki da bukatunsa ba, wadanda aka gabatar domin neman kawo karshen goyon baya da taimakon da Liberiya take bai wa 'yan tawayen R.U.F. na kasar Saliyo.

An fara kafa wannan takunkumi shekara guda da ta shige domin dakile fasa-kwabrin duwatsun lu'ulu'u da makamai a Saliyo, makwabciyar Liberiya.

Gwamnatin Liberiya tayi kira ga Kwamitin Sulhun da ya dage wannan takunkumi, tana mai cewa yana yin illa ga talakawan kasar.

A watan da ya shige, wani kwamitin kwararru na MDD ya bada rahoton cewa Liberiya ta sha karya takunkumin makamai.

XS
SM
MD
LG