Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Gana Da Firayim Minista Ariel Sharon A Yau Talata - 2002-05-07


Wani lokaci a yau talata, shugaba Bush zai gana da Firayim Ministan Isra'ila, Ariel Sharon, a fadar White House, domin tattaunawar da za ta mayar da hankali ga batun rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

Mr. Sharon ya iso nan Amurka da wani kundin bayanan da Isra'ila ta ce, suna alakanta jagoran Falasdinawa, Malam Yasser Arafat, da ta'addanci.

Yayin da Mr. Sharon yake son a mayar da Malam Arafat saniyar-ware, a kokarin samun zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya, jami'an Amurka sun yi nunin cewa, Malam Arafat yana da goyon bayan Falasdinawa, don haka dole ne Isra'ila ta yi hulda da shi.

A taron na yau, fadar White House ta ce Mr. Bush yana son mayar da hankali ga yadda za a raya shirin samun zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.

A jiya litinin ne, sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya gana da Mr. Sharon da Sarki Abdullah na Jordan da kuma ministan harkokin wajen Sa'udiya, domin tattaunawa gameda wani shirin yin taron kasa da kasa kan bukatar samun zaman lumana a wannan yanki.

XS
SM
MD
LG