Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Isra'ila 15 Sun Mutu A Harin Kunar-Bakin-Wake - 2002-05-08


Mutane akalla 15 sun mutu, wasu fiye da 50 kuma suka ji rauni a harin kunar-bakin-waken da wani Bafalasdine ya kai jiya talata a birnin Rishon Letzion na Isra'ila.

Dan harin ya tarwatsa kansa a cikin wani dakin kwallon tebur na "Pool" dake cike da mutane, har jinkar dakin ya fado ya danne wasu daga cikin wadanda abin ya shafa. 'Yan sanda da ma'aikatan agaji na Isra'ila, sun kwarara zuwa wurin da aka kai wannan hari a kudu da birnin Tel Aviv.

Kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas ta dauki alhakin kai harin.

Wani jami'i a ofishin firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila, ya bayyana lamarin a zaman wani sabon mummunan harin kan Isra'ila. David baker, ya ce wannan harin ya nuna cewa har yanzu, a ta bakinsa, "majalisar mulkin kan Falasdinawa ba tayi watsi da aniyarta ta kisan kai ba."

Shugabannin Falasdinawa sun bada sanarwar yin tur da harin. Sanarwar ta ce harin yana taimakawa ikirarin da Isra'ila take yi cewa Falasdinawa ba su son zaman lafiya.

Wannan shine harin kunar-bakin-wake na farko da Falasdinawa suka kai, tun ranar 12 ga watan Afrilu, lokacin da wani mahari ya kashe mutane 6 a tsakiyar birnin Qudus.

Harin ya zo a daidai lokacin da Mr. Sharon da shugaba Bush suka fara tattaunawa a nan birnin Washington.

XS
SM
MD
LG