Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman China Da Misra Sun Fadi... - 2002-05-08


A bisa dukkan alamu, babu wanda ya tsira da ransa a cikin wani jirgin saman fasinja na China mai zirga-zirgar cikin gida, wanda ya fadi jiya talata a gabar arewa maso gabashin kasar.

Akwai mutane 112 a cikin wannan jirgi kirar MD-82, wanda ya tashi daga birnin Beijing kasa da sa'a guda kafin faduwarsa.

Wata tawagar bincike ta musamman, ta isa birnin Dalian mai tashar jiragen ruwa domin bin diddigin musabbabin wannan hadari.

Akwai jiragen ruwan aikin agaji su 30 dake yankin inda jirgin ya fadi cikin ruwa suna neman wadanda suka jikkata ko gawarwakinsu. Kamfanin dillancin labaran Xinhua, ya ce an gano gawarwaki kimanin 60 ya zuwa yanzu.

Kamfanin dillancin labaran an Xinhua, ya ce sadarwa ta katse a tsakanin jami'ai masu kula da zirga-zirgar jirage a sama da kuma wannan jirgi, a bayan da matukinsa ya fada musu cewa gobara ta tashi cikin dakin tuka jirgin.

A halin da ake ciki kuma, jami'an Misra sun ce mutane akalla 18 sun mutu, a bayan da wani jirgin saman fasinja na kamfanin "Egypt Air" wanda ya fadi a kusa da Tunis, babban birnin Tunisiya.

Jirgin, kirar "Boeing 737", yana kokari ne yayi saukar gaggawa a filin jirgin saman Tunis, a yayin da ake sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya. Maimakon sauka a wannan fili, jirgin ya fadi a wani wuri mai tuddai, nesa da filin jirgin.

Wani jami'in Tunisiya, ya ce ba don dabarar da matukin jirgin yayi ta hana jirgin yin bindiga ta hanyar yankewa da jefar da tankin man jirgin ba, to da yawan wadanda zasu mutu zai zarce haka nesa ba kusa ba.

Matukin jirgin yana cikin wadanda suka kubuta da rai. Mutane akalla 25 sun ji rauni, an kuma kwantar da su a asibiti.

XS
SM
MD
LG