Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Warware Rikicin Zabe A Tarayyar Tsibiran Comoros - 2002-05-08


Wani tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja a Comoros, Azaly Assoumani, ya zamo shugaban farko na sabuwar Tarayyar Comoros, wadda ta sake hade tsibirai uku na wannan kasa a karkashin gwamnati guda daya.

Sabuwar hukumar zabe ta kasar, ita ta bayyana wannan jiya (Laraba). Hukumar tayi watsi da kukar da wasu 'yan takara biyu, tsohon kanar na soja Mahamoud Mradabi da dan siyasa, Sai Ali Kemal, suka shigar, har ma suka kauracewa zaben na ranar 14 ga watan Afrilu, suna masu fadin cewa an shirya yin magudi.

Hukumar ta ce an jefawa Kanar Assoumani kuri'u fiye da dubu 80. Ta ce wasu kuri'un fiye da dubu biyar kuma da aka jefawa sauran 'yan takarar biyu, an watsar da su saboda sunsaba ka'ida.

Har yanzu ba a ji ta bakin sauran 'yan takarar biyu ba. Amma kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci Mr. Mradabi yana fadin cewa babu dayansu da zai amince da sakamakon, kuma zasu matsa lambar da a gudanar ad sabon zabe.

Sabon tsarin mulkin Tarayyar Comoros, ya bai wa kowane guda daga cikin tsibirai uku na tarayyar, watau Grande Comore, da Moheli da kuma Anjouan, karin ikon cin gashin kai, ciki har da ikon da kowane tsibirin ke da shi na zaben shugabansa. Tsibiri na hudu na yankin, Mayotte, har yanzu yana karkashin mulkin mallakar Faransa.

XS
SM
MD
LG