Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ce Shugabanni Sun Kasa Kare Hakkin Yara Kanana - 2002-05-08


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya kaddamar da taron kolin farko na yara a hedkwatar majalisar, ta hanyar yin kira ga shugabannin kasashen duniya da dukkan manya balagaggu a fadin duniya da su daina kin kare hakkin yara kanana.

Mr. Annan ya ce dukkan yara suna da hakkin girma ba tare da sun yi fama da talauci, cuta, yaki da kuma jahilci ba. Ya ce shugabannin duniya sun nuna kashi sosai wajen kare hakkin yara kanana.

Akwai shugabannin kasashe fiye da 60 a cikin wakilan kasashe 180 dake halartar wannan taron na musamman, tare da wasu daruruwan yara kanana. Har ila yau akwai wakilan kungiyoyi masu zaman kansu a zauren taron.

Wata yarinya mai shekaru 13 'yar kasar Bolivia, ta gabatar da jawabi a wajen taron, inda ta kara jaddada irin ukubar da yara ke sha, da kuma yadda manya ke hada baki ta hanyar kyale su suna fuskantar bakar wahalar.

Sakataren kiwon lafiya na Amurka, Tommy thompson, ya jaddada muhimmanci janyo hankalin yara da su kauracewa yin jima'i, ko zina.

A yau alhamsi za a ci gaba da wannan taron kolin kwanaki uku, inda za a tattauna a kan ilmi, yaduwar cutar kanjamau ta AIDS, ko SIDA, da kuma yadda ake musugunawa yara kanana ta hanyar yin amfani da su a zaman sojoji, ko masu aiki kamar na bauta, ko kuma a zaman karuwai.

XS
SM
MD
LG