Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Kira Ga Shugabanni Masu Gaba Da Juna A Madagascar, Da Su Warware Rikicin Siyasa - 2002-05-09


Shugaba Bush na Amurka, yayi kira ga shugabannin Madagascar masu tsama da juna da su sake komawa kan teburin shawarwari domin warware rikicin siyasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi a watan Disamba.

A jiya (laraba) Mr. Bush ya roki Mr. Didier Ratsiraka da Mr. Marc Rabalomanana, da su tattauna domin samo abinda shugaban na Amurka ya kira "hanyar dindindin mai nagarta" ta kawo karshen rikicin.

Kowanne daga cikin mutanen biyu yana ikirarin cewa shine shugaban Madagascar. Kwanakin baya suka yarda zasu kafa gwamnatin rikon kwarya, yayin da za a sake kidaya kuri'un da aka jefa a zaben na watan Disamba.

A makon jiya, wata babbar kotu ta ayyana Mr. Ravalomanana a zaman wanda ya lashe zabe a bayan da aka sake kidaya kuri'un. An rantsar da shi a zaman shugaban kasar a ranar litinin, amma Mr. Ratsiraka ya ki yarda da sakamakon sake kidaya kuri'un, ya kuma bayyana bukin rantsar da sabon shugaban da aka yi a zaman wanda ya sabawa doka.

Mr. Bush ya ce yarjejeniyar da mutanen biyu suka cimma kwanakin baya a kasar Senegal, ta samar da ginshikin tabbatar da gaskiya tare da yin aiki tsakani da Allah, kuma ta hanyar dimokuradiyya domin warware wannan rikicin.

A yanzu, Senegal ta yi kira ga sassan biyu da su sake tattaunawa cikin mako mai zuwa a birnin Dakar, amma ba a san ko zasu je ba.

XS
SM
MD
LG