Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga Alamun Karshen Cirko-Cirkon Da Ake Yi A Bethlehem... - 2002-05-09


Ana kan shirye-shiryen fito da Falasdinawa daga majami'ar "Nativity" da Isra'ila ta kange. A bisa dukkan alamu, mashawarta sun cimma yarjejeniyar kawo karshen farmakin makonni biyar da Isra'ila take yi wa wurin ibadar na mabiya addinin Kirista.

Sojojin Isra'ila sun kakkafa fitilu masu haske da na'urorin sunsuna karfe a kewayen majami'ar, yayin da Falasdinawa a cikin majami'ar suka ce mashawarta suna tattauna tsarin yadda zasu fice daga ciki.

A karkashin yarjejeniyar, fararen hula kimanin 85 dake cikin majami'ar zasu yi tafiyarsu, yayin da 'yan kishin Falasdinu 26 zasu tafi Gaza domin fuskantar shari'a a kotunan Falasdinawa.

Wasu 'yan kishin Falasdinu su 13, wadanda Isra'ila ta kira "manyan 'yan ta'adda" kuma, zasu ci gaba da zama a cikin majami'ar, har sai an samu kasar da ta yarda ta karbe su. Italiya da Spain da Jordan duk sun ki yarda da bukatar karbar mutanen.

XS
SM
MD
LG