Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Bada Umurnin Soke Tashi Ko Saukar Dukkan Jiragen Sama Kirar B-A-C-1-11 - 2002-05-10


Nijeriya ta bada umurnin soke sauka ko tashin dukkan jiragen saman fasinja samfurin 1-11 kirar "British Aerospace", a bayan mummunan hadarin irin wannan jirgi ranar asabar da ta shige a birnin Kano, a arewacin Nijeriya.

Ministar kula da zirga-zirgar jiragen saman Nijeriya, Kema Chikwe, ta fada jiya alhamis cewar an kafa wata kungiya ta musamman da zata binciki hadarin na ranar asabar, da kuma yadda ake gudanar da ayyukan dukkan kamfanonin safarar jiragen sama masu zaman kansu a Nijeriya.

Da yawa daga cikin kamfanonin safarar jiragen saman Nijeriya, suna yin aiki da irin wannan jirgi samfurin B-A-C-1-11.

Har ila yau, Ms. Chikwe ta bada sanarwar cewa daga yanzu, gwamnati ba zata yarda tayi rajistar duk wani jirgin saman da ya wuce shekaru 22 da kerawa ba. Haka kuma, ma'aikatarta ta shawarci mutanen dake zaune a kusa da filayen sauka da tashin jiragen sama, da su yi wa kawunansu kiyamul-laili, su kaura, saboda tsaron lafiyarsu.

A ranar asabar da ta shige ne wani jirgin saman kamfanin E-A-S ya fadi kan wata unguwa mai dimbin mutane, a lokacin da yake kokarin tashi daga filin jirgin saman Kano, ya kashe mutane akalla 148.

XS
SM
MD
LG