Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Yabawa Shugaba Mbeki Na Afirka Ta Kudu... - 2002-05-10


Shugaba Bush ya buga waya ma shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu, jiya alhamis, domin bayyana goyon baya ga kokarin da yake yi na kawo karshen yakin basasar kasar Kwango-Kinshasa. Wakilin Muryar Amurka a fadar White House, ya aiko da rahoton cewa shugaba Mbeki yana karbar bakuncin wani sabon zagayen shawarwari na kungiyoyin kasar Kwango dake son fadada gwamnatin rikon kwaryar da ake shirin kafawa a kasar.

Shugaban na Afirka ta Kudu, ya fara gudanar da shawarwari a birnin Cape Town, domin fadada yarjejeniyar rarraba ikon da aka cimma a gefen taron tattaunawar da aka yi cikin watan da ya shige a birnin Sun City. Wancan yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamnatin shugaba Joseph Kabila na Kwango da 'yan tawayen dake samun goyon bayan Uganda, wadanda kuma ke rike da akasarin yankunan arewacin kasar, ba ta kunshi 'yan tawayen gabashin Kwango, wadanda su kuma ke samun goyon bayan kasar Rwanda ba.

Shugaba Mbeki yana ganawa da wadannan 'yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda, da kuma wasu jam'iyyun adawa da kungiyoyin jama'a kimanin 12 wadanda suka ki yarda su sanya hannu kan wancan yarjejeniyar.

Kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya ce shugaba Bush ya buga waya ma shugaba Mbeki jiya alhamis, domin gode masa saboda kokarin da yake yi ya zuwa yanzu, tare da karfafa masa guiwa kan ya ci gaba da wannan kokari, ko za a samu cimma shirin zaman lafiya da zai hada da dukkan sassan kasar masu gaba da juna.

Ya ce, shugaban na Amurka, ya godewa shugaba Mbeki saboda jagorancin da ya nuna wajen karbar bakuncin tattaunawa a tsakanin sassan kasar Kwango Kinshasa a birnin Sun City. Mr. Fleischer, ya ce shugaban ya bayyana goyon bayansa ga kokarin da shugaba Mbeki yake ci gaba da yi cikin makon nan a birnin Cape Town, domin taimakawa sassan na Kwango wajen cimma yarjejeniya kan yadda za a kafa gwamnatin rikon kwarya.

A can gefe guda kuwa, an yi, ana kuma yin, fargabar cewa rashin shigar da 'yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda a cikin yarjejeniyar, yana iya haddasa sabon fada a yakin basasar da aka yi shekaru hudu ana yi a Kwango.

Yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin gwamnati da 'yan tawayen da Uganda take marawa baya ta bai wa dukkan sassan manyan mukamai cikin gwamnatin rikon kwarya da za a kafa nan gaba, kafin a gudanar da zaben da aka yi imanin cewa shine na farko da za a gudanar tsakani da Allah tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga Belgium a shekarar 1960.

Mr. Fleischer ya ce shugaba Bush yayi imanin cewa hanya guda daya tak ta warware matsalar da ake fama da ita a Kwango Kinshasa ita ce ta cimma wata yarjejeniyar wadda zata kunshi dukkan sassan da suke da hannu a rikicin na Kwango.

Mr. Fleischer ya ce shugaba Bush ya lura cewa Afirka ta Kudu tana iya fara sabon gini a kan ci gaban da aka samu a tsakanin gwamnatin Kwango Kinshasa, da wasu daga cikin sassan kasar, sannan kuma shugaban na Amurka ya kara jaddada bukatar cimma yarjejeniyar da zata kunshi kowa da kowa.

Afirka ta kudu, ta ce dukkan sassan na Kwango Kinshasa, ciki har da gwamnati, sun yarda cewa ya kamata a ci gaba da wannan tuntubar juna a gefe da ake yi a yanzu. Amma kuma, gwamnatin ta Kwango Kinshasa, da 'yan tawayen dake samun goyon bayan Uganda, duk sun kauracewa tattaunawar da aka yi jiya alhamis.

XS
SM
MD
LG