Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tsarin Mulkin Kasar Mali Ta Yanke Hukumci Kan Zagaye Na Biyu Na Zaben Shugaban Kasa - 2002-05-10


Kotun tsarin mulkin Mali, ta ce tsohon shugaban mulkin sojan kasar, Janar Amadou Toumani Toure, zai kara da Soumaila Cisse, dan takarar jam'iyyar dake mulkin kasar, a zagaye na biyu na zaben fidda gwani wanda za'a yi jibi lahadi idan Allah Ya kai mu.

Sakamakon da kotun ta bada a jiya alhamis, ya zo daya da sakamakon farko da ofishin ministan cikin gidan kasar ya bada tun ranar juma'ar da ta gabata.

Kafin ta bada sakamakon ta na karshe, kotun tsarin mulkin, wadda aka dora wa nauyin tabbatar da sahihancin sakamakon zagayen farko na zaben, ta yi watsi da kimanin rubu'i daya na kuri'un da aka kada, tana mai cewa suna cike da kura-kurai.

Hukumar zaben kasar mai zaman kanta, da kuma wasu jam'iyyun adawa masu yawa, sun bayyana shakkunsu game da adalcin zaben a zagayen farko.

Dan takarar da ya zo na ukku a zaben, kuma tsohon firayim ministan kasar Mali, Ibrahima Keita, ya gabatar da korafi ga kotun tsarin mulkin, yana mai zargin cewa an tafka gagarumin magudi da kuma sarrafa kuri'u yadda aka ga dama. Sannan kuma cibiyar ci gaban demokradiya ta Jimmy Carter, tsohon shugaban Amurka, dake nan Amurka ta bayyana cewa jami'anta da suka je kallon zaben, sun ji takaici saboda an hana su ganin yadda aka kidaya kuri'un da aka kada a zagayen farko.

A cikin watan jiya na Afrilu ne, 'yan kasar Mali da suka isa munzulin zabe su fiye da miliyan biyu suka kada kuri'un zaben shugaban kasarsu daga cikin 'yan takara 24.

Dan takarar da yayi nasara a zagaye na biyu, zai maye gurbin shugaban kasar na yanzu, Alpha Oumar Konare, wanda kundin tsarin mulkin kasar Mali ya haramtawa neman shugabancin kasar a wa'adi na ukku.

XS
SM
MD
LG