Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Masu Kishin Falasdinu Sun Fito Daga Majami'ar Bethlehem - 2002-05-10


Za a dauki 13 daga cikin Falasdinawa 'yan kishin kasa da suka fito daga cikin majami'ar "Nativity" bayan sun shafe makonni 5 a ciki, zuwa tsibirin Cyprus nan gaba a yau Jumma'a.

Yau da sanyin safiya 'yan kishin Falasdinun suka fara fitowa daga cikin majami'ar dai-dai da dai-dai, daga inda sojojin Isra'ila suka yi musu rakiya zuwa cikin wata motar safa da ta dauke su zuwa filin jirgin saman Ben Gurion. A nan ne zasu shiga cikin wani jirgin saman soja na Britaniya zuwa Cyprus.

An samu nasarar warware wannan cirko-cirko jiya alhamis, a lokacin da Cyprus ta yarda ta karbi 'yan kishin Falasdinun na wani dan lokaci, daga baya kuma, za a tura su zuwa kasashen yammacin turai dabam-dabam da suka yarda kan zasu karbe su.

A ranar litinin jami'an Tarayyar Turai zasu yanke shawara kan inda za a tura mutanen 13. Daga cikin kasashen da ake sa ran zsasu karbe su akwai Spain, da Italiya da kuma Girka.

Za a tura wasu 'yan bindigar su 26 zuwa zirin Gaza. Za a kuma saki wasu su fiye da 80.

Mutane kimanin 200 sun nemi mafaka cikin majami'ar a lokacin da sojojin Isra'ila suka kai farmaki cikin Bethlehem a ranar 2 ga watan Afrilu. Wasu mutanen sun samu sukunin fita, yayin da 'yan kwanton-bauna na Isra'ila suka kashe wasu da dama.

XS
SM
MD
LG