Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Wucin Gadi Na Isra'ila Sun Fara Komawa Gida... - 2002-05-13


Rundunar sojan Isra'ila ta tura wasu daga cikin sojojin wucin-gadinta gida. Tun farko an sanya wadannan sojoji cikin damara saboda wani farmakin sojan da aka shirya kaiwa cikin zirin Gaza.

Ministan tsaron Isra'ila, Binyamin Ben-Eliezer, ya shaidawa gidan telebijin na CNN jiya lahadi cewa an dage shirin kai farmakin, amma kuma ya ce Isra'ila tana da 'yancin maida martanin duk wani harin da Falasdinawa suka kai mata.

Mazauna zirin Gaza sun fara zaman jiran tsammanin wannan farmakin na Isra'ila, tun daga harin bam na kunar-bakin-waken da ya kashe 'yan Isra'ila 15 a makon da ya shige.

Amma majiyoyin sojan Isra'ila sun ce kwamandoji sun damu da irin yawan rayukan fararen hula da za a iya rasawa a zirin Gaza wanda ke shake da jama'a, da kuma yayata wannan farmakin da kafofin labarai suka yi tun kafin a kai shi, abinda ya ce ya sa kowa ya san da shi.

Kafofin yada labaran Isra'ila kuma sun ce Amurka ta matsawa Isra'ila lamba a kan ta dakatar da kai farmakin.

XS
SM
MD
LG