Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Liberiya Sun Kai Hari Kusa Da Babban Birnin Kasar - 2002-05-13


'Yan tawayen dake yakar sojojin gwamnati a kasar Liberiya sun kai hari kan garin Klay, mai tazarar kilomita 40 a arewa maso gabas da Monrovia, babban birnin kasar.

Ministan tsaron Liberiya, Daniel Chea, ya gaskata rahotannin cewa 'yan tawaye sun kai hari kan garin Klay.

Fadan da ake gwabzawa a tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnati masu biyayya ga shugaba Charles Taylor, ya sa a cikin makon nan majalisar dokokin kasar ta kara tsawon wa'adin yin aiki da dokar-ta-bacin da Mr. Taylor ya ayyana cikin watan Fabrairu.

Cikin irin abubuwan da dokar ta tanada, har da bai wa sojojin gwamnati iznin shiga da binciken gidajen mutane.

Fada ya karu cikin 'yan makonnin nan a tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye masu neman hambarar da shugaba Taylor.

Mr. Taylor ya kafa dokar-ta-baci a watan fabrairu, a lokacin da 'yan tawayen kungiyar L.U.R.D. suka fara yin barazana ga babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG