Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Liberiya Suna Yin Sintiri A Babban Birnin Kasar... - 2002-05-14


Shugaba Charles Taylor na Liberiya ya roki jama'a da su kwantar da hankulansu a bayan da mazauna birnin Monrovia suka rude suka fara tserewa daga cikin babban birnin kasar, a sanadin harin da 'yan tawaye suka kai kusa da nan.

Shugaba Taylor ya fada a cikin wani jawabi ta gidan rediyo cewa dakarun tsaro suna sintiri cikin birnin na Monrovia, kuma ba zasu bari wani dan tawaye ya kusanci wannan birni ba. Mr. Taylor yayi rangadin Monrovia, inda harkokin yau da kullum suka tsaya cik jiya litinin.

Tun da fari a jiya litinin din, kararrakin bindigogin igwa da aka yi ta ji daga yankuna masu tazarar kilomita 25 daga Monrovia, sun sanya jama'a sun fara fargabar cewa 'yan tawaye sun dirkaki birnin.

Shugaba Taylor ya tabbatar da cewa 'yan tawayen kungiyar "L.U.R.D." sun kai hari garin da aka haife shi, Arthington, wanda ke arewa da Monrovia.

Mazauna birnin monrovia sun firgita, inda dalibai suka watse daga cikin makarantu, aka rufe kantuna, yayin da daruruwan mutane suka gudu daga cikin birnin suka doshi wasu unguwannin bayan gari.

A ranar lahadi 'yan tawayen suka ce sun kama garin Klay, mai tazarar kilomita 35 daga Monrovia, suka kuma ce sun doshi babban birnin.

'Yan tawayen masu cibiya a arewacin Liberiya, sun kaddamar da hare-harensu mafi muni kwanaki bakwai da suka shige a kyamfel na neman hambarar da shugaba Taylor.

An gwabza wasu daga cikin fadace-fadace mafi muni kusa da Gbarnga, inda shi kansa shugaba Taylor ya jagoranci masu tawaye da gwamnati a farkon shekarun 1990.

XS
SM
MD
LG