Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidaya Kuri'u A Kasar Saliyo - 2002-05-15


An rufe rumfunan zabe a fadin kasar Saliyo, a bayan babban zaben farko da aka gudanar tun bayan kawo karshen yakin basasar shekaru 10 a kasar.

An fara kidaya kuri'u, amma jami'ai sun ce za a dauki kwanaki da dama kafin a samu cikakken sakamako. Rahotannin farko sun ce shugaba Ahmed Tejan Kabbah yana taka rawar-gani sosai a wasu gundumomin da tuni aka kammala kidaya kuri'unsu.

Mr. Kabbah yana takara da wasu mutane 9 a wannan zabe. Ana sa ran zai lashe wa'adi na biyu cikin sauki.

Akasarin masu fashin baki sun ce mutumin da zai biyo bayan shugaban shine Ernest Koromo na jam'iyyar "All People's Congress."

Jami'ai sun ce an gudanar da zaben lami lafiya ba tare da wata babbar matsala ba. 'Yan sandan Saliyo da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun yi gadin rumfunan zabe. Tun ma kafin a bude rumfunan zaben da sanyin safiyar jiya talata, jama'a sun yi dafifi suka fara yin layi.

Masu jefa kuri'a su miliyan 2 da dubu 300 na kasar Saliyo, suna zaben sabon shugaba da kuma 'yan majalisar dokoki a wannan zaben da jam'iyyu da dama suke takararsa.

Mutane masu yawan gaske sun fito domin kada kuri'unsu.

XS
SM
MD
LG