Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Da Kofi Annan Sun Yi Tur Da Kokarin 'Yan Tawayen Liberiya... - 2002-05-16


Kwamitin Sulhun MDD, da kuma Babban Sakatare Kofi Annan, sun yi tur da kokarin 'yan tawaye na kwace mulki karfi da yaji a kasar Liberiya. Har ila yau sun yi kira ga kasashen duniya da su bada agaji domin taimakawa fararen hular da wannan rikici ya rutsa da su.

A cikin takardun sanarwa dabam-dabam da suka bayar jiya laraba, Kwamitin Sulhun, da kuma babban Sakataren sun ce sun damu sosai da halin jinkai da aka shiga a saboda kazancewar fada tsakanin sojojin gwamnatin Liberiya da na 'yan tawayen dake neman hambarar da shugaba Charles Taylor.

A ranar litinin, kungiyar 'yan tawayen da ake kira "L.U.R.D." a takaice, ta ce kilomita 25 ya rage mata ta shiga Monrovia, babban birnin kasar.

Mr. Annan yayi kira ga gwamnatin Liberiya da 'yan tawaye da su fara tattaunawa. Ya ce yana goyon bayan kokarin da Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, take yi na shiga tsakanin sassan biyu domin kawo karshen wannan fitina.

Yayi kira ga kasashen yankin da kada su bari a yi amfani da yankunan kasashensu wajen kai hare-hare kan wasu kasashen. Ana zargin cewa kasar Guinea, makwabciyar Liberiya, tana tallafawa 'yan tawayen LURD.

Haka kuma, Mr. Annan yayi kira ga kasashen duniya da su bada agajin gaggawa ga kungiyoyin dake gudanar da ayyukan jinkai a yankin.

A jiya laraba, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta ce 'yan hijiran kasar Liberiya su dubu 3 da 500 sungudu zuwa kasar Guinea a sanadin wannan fada. Hukumar ta ce wannan shine adadi mafi yawa na 'yan Liberiya da suka gudu a lokaci guda zuwa Guinea cikin shekaru da dama.

Jami'an MDD sun bayyana fargabar cewa wasu 'yan gudun hijiran su dubu 10 zasu bi sawun na farko.

XS
SM
MD
LG