Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Saliyo Na Yanzu Yana Kan Gaba A Kuri'un Da Aka Kidaya - 2002-05-16


Sakamakon farko da aka fara samu na babban zaben da aka gudanar a Saliyo, ya nuna cewa shugaba Ahmed Tejan Kabbah ya fara yin nisa ma abokan takararsa.

Mr. kabbah ya fuskanci 'yan takara 8, cikinsu har da na jam'iyyar RUF ta 'yan tawaye, a zaben farko da aka gudanar a kasar tun bayan da aka kammala yakin basasar shekaru 10. Rahotannin farko sun nuna cewa jam'iyyar dake karkashin tsoffin 'yan tawayen ba ta samun goyon bayan kirki ba, har ma a wuraren da take da karfi, kamar birnin Makeni na arewacin kasar.

Jami'an MDD sun ce an gudanar da zaben na ranar talata cikin lumana, kuma ba tare da tursasawa ba. Sai dai an samu rahotannin yin magudi, ciki har da inda aka ce yara kanana suna jefa kuri'a a rumfunan zaben dake can cikin karkara.

Jiya laraba a nan birnin Washington, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje, Lynn Cassel, ta ce Amurka tayi farin cikin cewa an yi kyamfe, aka kuma gudanar da zabe kusan ba tare da wani tashin hankali ba.

Ba a sa ran za a samu cikakken sakamakon zabe har sai gobe Jumma'a.

XS
SM
MD
LG