Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Labor Ta Isra'ila Ta Gabatar Da Nata Ra'ayin kan Zaman Lafiya - 2002-05-16


Shugaban jam'iyyar Labor ta kasar Isra'ila, ya gabatar da shirin zaman lafiya, wanda ya tanadi cewa Isra'ila zata mika wasu sassan yankin Yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Qudus ga 'yantacciyar kasar Falasdinu da za a kafa nan gaba.

Benjamin Ben-Eliezer ya ce ya hangi kafa kasar Falasdinu wadda zata kunshi akasarin sassan yankin Yammacin kogin Jordan, da Zirin Gaza da kuma yankunan Larabawa na gabashin birnin Qudus.

Shirin nasa zai mika hakkin kula da wurare masu tsarki dake gabashin birnin Qudus ga abinda ya kira "hukuma ta musamman." Za a tsara yadda za a aiwatar da wannan a tattaunawar da za a yi a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Shirin na shugaban jam'iyyar Labor ya sha bambam sosai da na jam'iyyar Likud mai mulkin kasar Isra'ila. A makon jiya, jam'iyyar ta Likud ta amince da wani kuduri wanda ya ki yarda da duk wani ra'ayin kafa kasar Falasdinu.

Mr. Ben-Eliezer dai shine ministan tsaro a gwamnatin karo-karo ta Isra'ila. Ya gabatar da ra'ayoyin nasa ne ga Kwamitin zartaswar jam'iyyar Labor, wanda ke tattauna shawarwarin cimma zaman lafiya da wasu batutuwan kafin zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

XS
SM
MD
LG