Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Leken Asirin Amurka ba Su Da Takamammiyar Barazana Ta Hare-Haren 11 Ga Watan satumba... - 2002-05-17


Mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan harkokin tsaron kasa, Condoleeza Rice, ta ce hukumomin leken asirin Amurka suna da masaniyar cewa ana yin wasu 'yan kulle-kulle kafin ranar 11 ga watan Satumba.

Amma kuma ta ce babu wata alamar da aka gani cewar 'yan ta'adda zasu kara jiragen a jikin Cibiyar Cinikayya ta Duniya da hedkwatar ma'aikatar tsaro ta Pentagon.

Wannan furuci nata na jiya alhamis ya zo a bayan da fadar White House ta ce an shaidawa shugaba Bush kafin ranar 11 ga watan Satumba cewa tana yiwuwa magoya bayan Osama bin Laden zasu yi fashin jiragen saman fasinja.

Ms. Condoleeza Rice ta ce gargadin da aka samu ya maida hankali ne kan fashin jirgi kamar yadda aka saba gani, inda 'yan ta'adda zasu yi fashin jirgin su ce ga bukatunsu a biya musu.

Ta ce Hukumar Binciken manyan laifuffuka ta Tarayya ta Amurka, FBI, ta gargadi kamfanonin safarar jiragen sama, amma kuma gargadin babu wani abu takamamme a ciki da zai hana abkuwar hare-haren 11 ga watan satumba.

'Yan majalisar dokokin Amurka sun ce suna son su san abinda gwamnati ta sani kafin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu uku.

XS
SM
MD
LG