Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Yanke Shawara Kan Wuraren Da Za A Tura Kusan Dukkan Falasdinawa - 2002-05-20


Jami'an kasar Spain sun ce Tarayyar Turai ta yanke shawarar inda zata tura Falasdinawa 12 daga cikin guda 13 da Isra'ila ta tilastawa yin gudun hijira a farkon watan nan, bayan da aka jima ana yin cirko-cirko a majami'ar "Nativity" dake birnin Bethlehem.

An bada sanarwar cimma daidaituwa jiya lahadi, a bayan da aka yi kwana da kwanaki ana tattauna matsayin wadannan Falasdinawa, da kuma ainihin wuraren da za a tura su.

Jami'ai a birnin Madrid sun ce Spain da Italiya zasu karbi Falasdinawa uku-uku; Girka da Ireland zasu karbi bibbiyu; yayin da kowacce daga cikin Portugal da Belgium zata karbi Bafalasdine guda.

Ba a san inda za a tura Bafalasdine na 13 ba.

'Yan kishin Falasdinun su 13 suna zaune a wani hotel dake bakin teku a kasar Cyprus, inda ake gadinsu dare da rana, tun lokacin da sojojin Isra'ila suka kawo karshen farmaki a birnin Bethlehem ranar 10 ga watan nan na Mayu.

Isra'ila ta ce 'yan kishin Falasdinun su 13 'yan ta'adda ne.

XS
SM
MD
LG