Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata jaridar Britaniya Ta Samo Faifan Bidiyo Na Osama Bin Laden - 2002-05-20


Jaridar "Sunday Times" ta Britaniya, ta ce ta samu wani faifan bidiyo dake dauke da hoton Osama bin Laden maras tsawo, wanda watakila cikin watanni biyun da suka shige aka dauke shi.

Jaridar ta ce an samu wannan faifan bidiyon ne daga wani kamfanin dillancin labaran Islama dake Britaniya, wanda shi kuma ya ce an shaida masa cewa an dauki wannan hoto na bin Laden ne a cikin watan Maris.

Jaridar ta ce faifan bidiyo ya nuna Osama bin Laden ya ramae sosai, kuma fuskarsa ta dushe, yana zaune a karkashin inuwar wata bishiya, yana magana kan mutuwar shahada. Har ila yau, yayi gargadin cewa kungiyarsa ta al-Qa'ida zata kai hari kan duk wata kasar da ta goyi bayan Amurka ko Isra'ila.

Jaridar Times ta ce da alamun an dauki wannan hoton bidiyo da yamma cikin bazara, lokacin da ciyayi ta ganyayyki ke yin toho, amma kuma ba a san ko a ina ne ba.

XS
SM
MD
LG